11 Yuli 2021 - 12:48
Tsohon Babban Hafsan Hafsoshin ‘Isra’ila’ Ya Ja Kunnen Gwamnatin ‘Isra’ilan’ Kan Hatsarin Makaman Hizbullah

Tsohon babban hafsan hafsoshin sojojin Isra’ila, Janar Gadi Eisenko, ya ja kunnen ‘Isra’ilan’ dangane da hatsarin da makaman ƙungiyar Hizbullah ta ƙasar Labanon suke da shi ga haramtacciyar ƙasar.

ABNA24 : Janar Eisenko ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da yayi da jaridar Jerusalem Post ta ‘Isra’ilan’ inda ya bayyana cewar ƙungiyar ta Hizbullah tana da dubun dubatan rokoki da makamai masu linzami masu cin dogon zango da suke zama babbar barazana ga ‘Isra’ila’.

Tsohon babban hafsan hafsoshin ‘Isra’ilan’ yayi kirdadon cewa duk wani babban yaƙi da zai ɓarke tsakanin ‘Isra’ila’ da Hizbullah ɗin, yahudawan za su ji jiki don kuwa za su zauna cikin rami na tsawon sannan kuma Isra’ilan za ta fuskanci gagarumar hasara.

Tsohon Janar ɗin na ‘Isra’ila’ ya ƙare da cewa Hizbullah ɗin tana da rokoki da makamai masu linzami da suka kai dubu 150, wanda ya ce hakan babbar barazana ce ga haramtacciyar ƙasar.

A yaƙin 2006 dai ‘Isra’ilan’ ta ƙaddamar kan Hizbullah ɗin, dakarun Hizbullah ɗin sun ɗanɗana wa yahudawan kuɗa lamarin da ya sanya Isra’ilan neman a tsagaita wuta lamarin da ya ba wa ƙungiyar nasara a kan gwamnatin sahyoniyawan.

342/